- Gargadarwa daga ketare iyakar shari'a a girmamawa da yabo; domin cewa hakan yana kaiwa zuwa ga shirka.
- Abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi gargadi akan sa ya afku a cikin wannan al'ummar, sai wasu mutane suka wuce gona da iri a Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, wasu mutanen kuma a iyalan gidansa, wasu mutanen kuma a waliyyai, sai suka fada a cikin shirka.
- Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya siffanta kansa da cewa shi bawan Allah ne; dan ya bayyana cewa shi bawa ne wanda yake bauta ga Allah, ba ya halatta a juyar masa da wani abu daga abinda Ubangiji Ya kebanta da shi.
- Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya siffanta kansa da cewa shi Manzon Allah ne abin aikowa daga wurin Allah to gasgata shi da binsa ya wajaba.