Ya Ubangiji Kai ne aminci, kuma aminci daga gareka yake, Ka ɗaukaka ya ma’abocin girma da karamci
Daga Sauban, Allah Ya yarda da shi: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan ya sallame daga sallah yana neman gafara sau uku, ya kuma ce: Ya Ubangiji Kai ne aminci, kuma aminci daga gareka yake, Ka ɗaukaka ya ma’abocin girma da karamci . Walid ya ce: Na cewa Awza’i: Ya neman gafarar yake? Ya ce: Za ka ce ne:
Ina neman gafarar Allah, ina neman gafarar Allah,
Muslim ne ya rawaito shi
Bayani
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana cewa idan ya kammala sallarsa; Ina neman gafar Allah, Ina neman gafarar Allah, Ina neman gafarar Allah.
Sannan sai ya girmama Ubangijinsa, ya ce: "Ya Ubangiji Kai ne aminci, kuma aminci daga gareKa yake, Ka girmama ya ma’abocin girma da karamci".
Shi Allah tsarkakke ne, kuma cikakke ne a siffofinsa, kuma Ya tsarkaka daga barin kowanne aibu da tawaya, kuma ka nemi waraka daga dukkan sharri duniya da lahira daga wajenSa ba daga wani ba, Shi Allah alheranSa sun yawaita a duniya da lahira, Ma’abocin girma da kyautatawa ne.
Hadeeth benefits
Ana son neman gafara bayan kammala sallah, da kuma dawwama a kan hakan.
Ana son neman gafara domin cike tawaya a ibada, da ɗori na kasawa a ibadar.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others