- Kwaɗaitarwa akan yin wanka ranar Juma'a, kuma yana kasancewa ne kafin tafiya zuwa sallah.
- Falalar gaggawa zuwa sallar Juma'a daga farkon sa'o'in yini.
- Kwaɗaitarwa akan gaggawa ga ayyuka na gari.
- Halartowar mala'iku sallar Juma'a da sauraransu ga huɗuba.
- Mala'iku suna ƙofofin masallatai, suna rubuta masu shigowa, na farko sai mai beye da shi, a zuwa sallar Juma'a.
- Ibnu Rajab ya ce: Faɗinsa: "Wanda ya yi wanka ranar Juma'a, sannan ya tafi" yana nuni akan cewa wankan da ake so dan Juma'a farkonsa shi ne bullowar alfijir, ƙarshensa kuma tafiya zuwa Juma'a.