- Falalar ranar Juma'a akan sauran kwanukan mako.
- Kwaɗaitarwa akan yawaita ayyuka na gari a cikin ranar Juma'a, da yin tanadi dan samun rahamar Allah - Maɗaukakin sarki -, da tunkuɗe azabarsa.
- Waɗannan keɓantattun abubuwan na ranar Juma'a da aka ambace su a cikin Hadisin, wasu malam sun ce: Su ba dan ambatan falalar ranar Juma'a ba ne; domin fitar da (Annabi) Adam da tashin Alkiyama ba'a ɗaukarsu falala. Wasu malaman su ka ce: Kai dukkaninsu falala ce, kuma fitar (Annabi) Adam sababin samun zuriya ne kamar manzanni da annabawa da salihai, tsayuwar Alkiyama kuwa sababin gaggauto da sakamakon salihai ne da samun su ga abinda Allah Ya tanadar musu na karamomi.
- An ambaci wasu keɓantattun abubuwa daban ga ranar Juma'a, banda abinda aka ambata a cikin wannan riwayar, daga cikinsu: A cikinta ne aka karɓi tuban (Annabi) Adam, kuma acikinta ne aka ɗauki ransa, kuma aciknta akwai wani (Takaitaccen) lokaci bawa mumini ba zai dace da shi ba yana sallah (Addu’a) yana roƙon Allah wani abu ba sai Ya amsa masa.
- Mafificin yini a shekara ranar Arfa, (wasu malaman) suka ce: Ranar babbar sallah, kuma mafificin kwanukan mako ranar Juma'a, mafificin darare kuma daren Lailatul Kadr.