- Karhancin barin tsayuwar dare, kuma cewa hakan da sababin Shaiɗan ne.
- Tsoratarwa daga Shaiɗan wanda yake zama ga mutum a kan kowace hanya; dan ya tsare tsakaninsa da tsakanin ɗa'ar Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
- Ibnu Hajar ya ce: Faɗinsa: (Bai tashi zuwa sallah ba) abin nufi jinsi, kuma zai iya ɗaukar alƙawari, kuma ana nufin sallar dare ko (sallar) farillah da shi.
- Al-Ɗaibi ya ce: An keɓanci kunne da anbato, duk da ido yafi dacewa da bacci, dan yin nuni zuwa nauyin bacci, domin cewa kunnuwa sune magangarar farkawa, kuma an keɓanci fitsari; domin cewa shi ya fi sauƙin shiga a cikin ciki, kuma mafi saurin zarcewa a cikin jijiyoyi, sai ya gadar da kasala a cikin dukkan gaɓɓai.