- Kwaɗaitarwa akan gaggawar zuwa sallar jam’i da halartarta, kuma kada ya yi sallah a bayan sawu shi kaɗai dan kada ya bijirar da sallarsa ga ɓaci.
- Ibnu Hajar ya ce: Wanda ya fara sallah shi kaɗai a bayan sawu sannan ya shiga cikin sawu kafin ɗagowa daga ruku'u to sakewa ba ta wajaba gare shi ba, kamar yadda yake a cikin hadisin Abu Bakrata, inba haka ba to yana wajaba abisa gamewar hadisin Wabisah.