- Mai sallah idan ya yi kokwanto a cikin sallarsa, sai kuma bai iya rinjayar da ɗayan abu biyun gare shi ba, to anan ya watsar da kokwanton ya yi aiki da yaƙini, shi ne mafi ƙaranci, sai ya cika msallarsa ya yi sujjada kafin ya yi sallama, sannan ya yi sallama.
- Waɗannan sujjadun biyu hanya ce zuwa gyara sallah, da mayar da Shaiɗan a taɓe ƙasƙantacce abin nisantarwa daga manufarsa.
- Kokwanton da yake cikin Hadisin shi ne kaikawo ba tare da rinjayarwa ba, idan an sami zato kuma ya yi rinjaya sai a yi aiki da shi.
- Kwaɗaitarwa akan yaƙar waswasi da tunkuɗe shi ta hanyar ruko da umarnin shari'a.