- Muhimmancin kyautata sallah da zuwa da rukunanta da nutsuwa da ƙanƙar da kai.
- Siffanta wanda ba ya cika ruku'unsa da sujjadarsa da cewa shi ɓarawo ne; kyamatar hakan ne gami da faɗakarwa a kan haramcinsa.
- Wajabcin cika ruku'u da sujjada a sallah da daidaito a cikinsu.