/ Wannan wani Sahiɗan ne ana ce masa khinzab, idan ka ji shi ka nemi tsarin Allah daga gare shi, ka yi tofi a hagunka sau uku

Wannan wani Sahiɗan ne ana ce masa khinzab, idan ka ji shi ka nemi tsarin Allah daga gare shi, ka yi tofi a hagunka sau uku

Daga usman ɗan Abul Aas - Allah Ya yarda da shi -: Lallai ya zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai haƙiƙa Shaiɗan ya shiga tsakanina da sallata da kuma karatuna, yana rikitar da ni, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wannan wani Sahiɗan ne ana ce masa khinzab, idan ka ji shi ka nemi tsarin Allah daga gare shi, ka yi tofi a hagunka sau uku", sai ya ce: Sai na aikata hakan sai Allah Ya tafiyar da shi daga gareni.
Muslim ne ya rawaito shi

Bayani

Usman ɗan Abul Aas - Allah Ya yarda da shi - ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah lallai cewa Shaiɗan haƙiƙa ya shiga tsakanina da sallata ya hanani khushu'i a cikinta, ya cakuɗa min karatuna ya sa ni kokwanto a cikinta, Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Wannan Shaiɗan ne ana ce masa Khinzab, idan ka ka sami hakan, kuma ka ji shi ka nemi mafaka a wurin Allah, ka nemi tsarin Allah daga gare Shi, ka yi tofi a hagunka tare da yawu kaɗan sau uku, Usman ya ce: Sai na aikata abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umarce ni da shi, sai Allah Ya tafiyar da shi daga gareni.

Hadeeth benefits

  1. Muhimmnacin khushu'i da halartowar zuciya a sallah, kuma cewa Shaiɗan yana ƙoƙari a sa ruɗu da kokwanto a cikinta.
  2. An so neman tsarin Allah daga Shaiɗan a yayin waswasinsa a sallah, tare da tofi a hagu sau uku.
  3. Bayanin abin da sahabbai - Allah Ya yarda da su - suke a kansa na komawarsu zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin abin da yake faruwa garesu na matsaloli har ya warware musu su.
  4. Rayuwar zuciyar sahabbai, kuma cewa himmarsu (damuwarsu) ita ce lahira