Babu sallah in akwai abinci a gaban [mutum], ko kuma a lokacin yana matse najasa biyu, (fitsari da bayan gida)
Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Babu sallah in akwai abinci a gaban [mutum], ko kuma a lokacin yana matse najasa biyu, (fitsari da bayan gida).
Muslim ne ya rawaito shi
Bayani
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya hana sallah in a wurin akwai abincin da ran mai sallah yake sha'awarsa, kuma zuciyarsa take rataye da shi.
Haka nan ya hana sallah tare da matse najasa biyu - su ne fitsari da bahaya -, saboda shagaltuwa da matse najasar.
Hadeeth benefits
Ya kamata ga mai sallah ya nisantar da dukkanin abin da zai shagaltar da shi a cikin sallarsa kafin ya shiga cikin sallar.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others