- Lallai cewa bin Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana daga biyayyar Allah, kuma saɓa masa yana daga saɓawa Allah.
- Bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana wajabta aljanna, saɓa masa kuma yana wajabta wuta.
- Albishir ga masu biyayya daga cikin wannan al'ummar, kuma cewa su dukkaninsu za su shiga aljanna, sai wanda ya saɓawa Allah da Manzonsa.
- Tausayinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a
- gareshi - ga al'ummarsa, da kwaɗayinsa a kan shiriyarsu.