Ni ne mafi wadatar abokanan tarayya daga shirka, duk wanda ya aikata wani aiki ya hada ni da wani a aikin to Zan bar shi da shirkarsa
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah - alherinSa ya yawaita Ya girmama - Ya ce: Ni ne mafi wadatar abokanan tarayya daga shirka, duk wanda ya aikata wani aiki ya hada ni da wani a aikin to Zan bar shi da shirkarsa".
Muslim ne ya rawaito shi
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana sanar da cewa Allah - alherinSa ya yawaita Ya girmama - Ya ce: Lallai cewa Shi ne mafi wadatar abokanan tarayya game da shirka, to Shi ne Mawadaci daga dukkanin komai, kuma cewa mutum idan ya aikata wani aiki na biyayya kuma ya sanya shi ga Allah da kuma wanin Allah; to Zai bar shi ba zai karba daga gare shi ba, kuma Ya miyarwa da mai shi; To tsarkake aiki yana wajaba ga Allah - Madaukakin sarki -; domin cewa shi Allah tsarki ya tabbatar maSa ba ya karba sai abinda ya zama tsarkakakke ga zatinsa Mai girma.
Hadeeth benefits
Gargadi daga shirka da dukkanin ire-irenta; kuma cewa ita tana hana karbar aiki.
Jin wadatar Allah da Girmansa yana daga abinda yake taimakawa ga ikhlasi a cikin ayyuka.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others