Lalle Allah Yana yarda da bawanda idan ya ci abin ci, yana gode masa a kai, ko in ya sha abin sha sai ya gode masa akan hakan
Daga Anas Ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Lalle Allah Yana yarda da bawanda idan ya ci abin ci, yana gode masa a kai, ko in ya sha abin sha sai ya gode masa akan hakan.
Muslim ne ya rawaito shi
Bayani
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana godiyar da bawa ya ke yi wa Ubangijinsa a kan falalarSa da ni’imarSa suna cikin al’amuran da ake samun yardar Allah da su, idan ya ci abin ci sai ya ce: Na gode wa Allah. Idan ya sha abin sha sai ya ce: Alhamdulillah.
Hadeeth benefits
Karamcin Allah Mabuwayi, haƙiƙa shi ne ya ba da arziƙi, kuma yake yarda da a gode masa.
Yardar Allah ana samunta da abu mafi sauƙi, kamar godiya ga Allah bayan ci da sha.
Yana daga cikin ladubban ci da sha: Godiya ga Allah maɗaukaki bayan ci da sha.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others