- Daga ladubban ci da sha (akwai) ambaton Allah a farkonsa.
- Sanar da yara ladubba, musamman ma waɗanda ke ƙarƙashin kulawar mutum.
- Tausayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da yalwar ƙirjinsa a koyar da yara da ladabtar da su.
- Daga ladubban abinci akwai cin abin da ke gaban mutum, sai dai idan ya kasance nau'uka ne da yawa, to, yana da damar da zai ɗauki wanda ya so.
- Lazimtar sahabbai da abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ladabtar da su da shi, hakan abin fahimta ne daga faɗin Umar: Hakan bai gushe (irin) cin abincina ba bayan nan.