Idan ɗayanku zai ci; to, ya ci da damansa, idan zai sha; to, ya sha da damansa, domin cewa Shaiɗan yana ci da hagunsa, kuma yana sha da hagunsa
Daga Dan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku zai ci; to, ya ci da damansa, idan zai sha; to, ya sha da damansa, domin cewa Shaiɗan yana ci da hagunsa, kuma yana sha da hagunsa".
Muslim ne ya rawaito shi
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana umarni cewa musulmi ya ci ya sha da hannunsa na dama, kuma yana hani daga ci da sha da hagu; domin cewa Shaiɗan yana ci kuma yana sha da shi (hannun hagu).
Hadeeth benefits
Hani daga kamamceceniya da Shaiɗan ta hanyar ci ko sha da hagu.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others