- Yana daga cikin ƙaƙalen da aka hana: Yawaita tambaya, ko ɗorawa kai abin da ba shi da iliminsa, ko tsanantawa a abinda Allah Ya sauƙaƙa a cikin sa.
- Ya kamata ga Musulmi ya koyawa kansa sauƙi, da rashin tsananta wa kai a magana, ko a aiki, a abin cinsa, ko abin sha, da maganganunsa da sauran ayyukansa.
- Musulunci addinin sauƙi ne.