- Wajibin dake kan mumini shi ne ya sanya wa mutane son Allah, ya kwadaitar da su alheri.
- Ya kamata ga mai kiran mutane zuwa ga Allah ya yi nazari cikin hikima a kan yadda zai isar da saƙon Musulunci zuwa ga mutane.
- Bushara tana haifar da farin ciki da karɓuwa da nutsuwa da abin da mai Da'awa ya ke gabatarwa ga mutane.
- Tsanantawa tana haifar da ƙyama da kuma juya baya da sanya shakku a maganar mai Da’awah.
- Yalwatuwar rahamar Allah ga bayinSa, da cewa Ya yardar musu da addini mai sauƙi da Shari’ah mai rangwame.
- Sauƙi da aka yi umarni da shi, shi ne wanda Shari’a ta zo da shi.