- Sauƙi da afuwar shari'ar Musulunci da tsakatsakiyarta tsakanin wuce gona da iri da kuma sakaci.
- Ya wajaba akan bawa ya aikata umarni gwargwadan ikonsa, ba tare da sakaci ko tsanantawa ba.
- Ya wajaba akan bawa ya zaɓi lokutan nishaɗi a cikin ibada, waɗannan lokuta ukun a keɓancesu sune mafi hutawar jiki dan yin ibada a cikinsu.
- Ibnu Hajar Al’Asƙalani ya ce: Kamar cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa matafiyi magana ne zuwa manufa, waɗannan lokuta ukun sune mafi daɗin lokutan matafiyi, sai ya faɗakar da shi akan lokutan kazar-kazar; domin matafiyi idan ya yi tafiyar dare da rana gaba ɗaya zai gajiya ya yanke, idan ya kintaci tafiya a cikin waɗannan lokuta masu nishaɗantarwa sai ya samu damar dawwama ba tare da wahala ba.
- Ibnu Hajar ya ce: Nuni a cikin wannan hadisin zuwa riƙo da sauƙi na shari'a, domin riƙo da azima a lokacin sauƙi zirfafawa ne, kamar wanda ya bar Taimama a lokacin gajiyawa daga anfani da ruwa sai anfani da shi ya kai shi zuwa faruwar wata cuta.
- Ibnul Munir ya ce; A cikin wannan Hadisin akwai alama daga alamomin Annabci, haƙiƙa mun ga mutane a gabaninmu sun ga cewa dukkan mai zirfafawa a Addini zai yanke, bawai ana nufin hana neman mafi cika a ibada ba cewa shi yana daga al'amura ababen yabo, kai hana wuce gona da iri mai kaiwa ne zuwa ƙosawa, kai zirfafawa a aikin nafila mai kaiwa ne zuwa ga barin abin da ya fi, ko fitar da farilla daga lokacinta kamar wanda ya kwana yana sallar dare gaba ɗayansa sai ya yi bacci daga sallar Asuba a cikin jam’i, ko zuwa lokacin hudowar rana sai lokacin farillar ya fita.