/ Lalle sassauci ba ya kasance wa a komai sai ya ƙara masa kyau, kuma ba a cire shi a komai sai ya aibanta shi

Lalle sassauci ba ya kasance wa a komai sai ya ƙara masa kyau, kuma ba a cire shi a komai sai ya aibanta shi

Daga Nana Aisha Allah Ya yarda da ita, matar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare ta ta ce: Lalle sassauci ba ya kasance wa a komai sai ya ƙara masa kyau, kuma ba a cire shi a komai sai ya aibanta shi.
Muslim ne ya rawaito shi

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana cewa rangwame da sauƙi da bi-sannu - sannu a magana da aiki suna ƙarawa abu kyau da cika da ƙaye, kuma nan ne ya fi cancanta mutum ya samu buƙatarsa. Rashin sassauci yana aibanta lamura yana muzanta su, kuma yana hana mai hakan cimma buƙatarsa, in kuma ya samu, to, da baƙar wahala ne.

Hadeeth benefits

  1. Kwaɗaitarwa a kan ɗabi’antuwa da halin sauƙaƙawa.
  2. Sauƙaƙawa tana ƙawata mutum, ita ce dalili na alheran duniya da lahira.