/ Wanda ya kare mutuncin ɗan uwansa Allah Zai kare fuskarsa daga wuta a ranar al-ƙiyama

Wanda ya kare mutuncin ɗan uwansa Allah Zai kare fuskarsa daga wuta a ranar al-ƙiyama

Daga Abu Al-darda - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gatreshi - ya ce: "Wanda ya kare mutuncin ɗan uwansa Allah Zai kare fuskarsa daga wuta a ranar al-ƙiyama".

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa wanda ya kare mutuncin ɗan uwansa musulmi a bayan idonsa ta hanyar hana zarginsa ko munana masa, to, lallai Allah Zai kareshi daga azaba a ranar al-ƙiyama.

Hadeeth benefits

  1. Hani daga magana a kan mutuncin musulmai.
  2. Sakamako yana kasancewa ne daga jinsin aiki, wanda ya kare mutuncin ɗan uwansa Allah Zai kareshi daga wuta.
  3. Musulunci addinin 'yan uwantaka ne da taimakekeniya a tsakanin ma'abotansa.