- Girman haƙƙin maƙoci da wajabcin kula da hakan.
- Ƙarfafawa a kan haƙƙin maƙoci da wasiyyarr da take hukunta larurar girmamashi da nuna soyayya da kyautatawa zuwa gareshi, da tunkuɗe cutarwa daga gareshi, da dubo shi a yayin rashin lafiya, da tayashi murna a yayin farin ciki, da yi masa ta'aziyya a yayin musiba.
- A duk lokacin da ƙofar maƙoci ta zama mafi kusa, to, haƙƙinsa ya zama mafi ƙarfi.
- Cikar shari'a a cikin abin da ta zo da shi na gyaran zamatakewa wajen kyautatawa maƙota da tunkuɗe cuta daga garesu.