- Banbance banbance mutane a matakan a imani.
- An so karfi a ayyuka; Domin yana faruwa ne daga fa'idar abinda ba ya faruwa da rauni.
- Mutum ya kamata ya yi kwadayi akan abinda zai anfane shi, kuma ya bar abinda ba zai anfane shi ba.
- Yana wajaba akan mumini ya nemi taimakon Allah a dukkanin al'amuransa, kuma kada ya dogara da kansa.
- Tabbatar da hukunci da kaddara, kuma shi ba ya kore kokari a sabubba da kokari a neman alkairai.
- Hani game da fadin "Da a ce" ta fuskar fushi a lokacin saukar musibu, da haramcin bijirewa hukunci da kaddara ga Allah - Madaukakin sarki -.