- Haramcin gina masallaci akan kabari, ko sallah a wurinsu, ko binne matattu a cikin masallaci; dan toshe kafa zuwa ga shirka.
- Gina masallaci akan kaburbura, da kafa hotuna a cikinsu, aikin yahudawa ne da kiristoci, kuma wanda ya aikata hakan, to hakika ya yi kamanceceniya da su.
- Haramcin rikon hotuna na masu rayuka.
- Wanda ya gina masallaci akan kabari ya kuma zana hotuna a cikinsa, to shi yana daga mafi sharrin halittar Allah - Madaukakin sarki -.
- Tsarewar da shari'a ta yi ga jinabin Tauhidi cikakkiyar tsarewa, ta hanyar toshe dukkanin hanyoyin da zasu kai zuwa ga shirka.
- Hani daga wuce gona da iri a salihai; domin cewa shi hanya ce ta fadawa cikin shirka.