- Hani daga wofintar da gidaje daga bautar Allah - Madaukakin sarki -a cikinsu.
- Hani daga tafiya dan ziyarar kabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -; domin cewa shi ya yi umarni da yin salati a gare shi kuma ya sanar da cewa shi yana isowa zuwa gare shi, kadai ana daure sirdi ne dan nufin masallaci da kuma sallah a cikinsa.
- Haramcin sanya ziyarar kabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - idi, ta hanyar maimaita ziyararsa ta kebantacciyar fuska a wani zamani kebantacce, hakanan ziyar kowanne kabari.
- Girman Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga Ubangijinsa, ta hanyar shara'anta yin salati da sallama a gare shi a kowanne zamani da kuma kowanne wuri.
- Yayin da cewa hanin game da sallah a wurin kaburbura hakika ya tabbata a wurin sahabbai; saboda haka Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya hana maida gidaje tamkar makabartun da ba'a sallah a cikin su.