- Ketare iyaka ta shari'a a cikin kaburburan Annabawa da salihan bayi ya maida su ana bauta musu koma bayan Allah, to kiyayewa daga hanyoyin shirka ya wajaba.
- Nufin kaburbura dan girmama su ba ya halatta da kuma yin ibada a gurin su duk yadda kusancin masu su yake ga Allah - Madaukakin sarki -.
- Haramcin gina masallatai akan kaburbura.
- Haramcin sallah a wurin da kaburbura suke koda bai yi gini ba saidai sallar jana'izar da ba'a yi wa gawar sallah ba kadai.