- Hani daga riƙon kaburburan Annabawa da salihai masallatan da za a dinga sallah a cikinsu; domin hakan hanya ce zuwa shirka.
- Tsananin himmatuwar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da kulawarsa a kan Tauhidi, da kuma tsoronsa daga girmama kaburbura; domin hakan yana kai wa zuwa shirka.
- Halaccin la'antar Yahudawa da Nasara, da wanda ya aikata irin aikinsu na gini a kan kaburbura da kuma rikonsu masallatai.
- Gini a kan kaburbura yana daga dabi’un Yahudawa da Nasara, a cikin Hadisin akwai hani daga kamanceceniya da su.
- Daga cikin riƙon kaburbura masallatai akwai yin sallah a wurinsu, da kuma zuwa garesu (wato kallonsu), ko da ba a gina masallaci ba.