/ Annamimi ba zai shiga aljanna ba

Annamimi ba zai shiga aljanna ba

Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa; "Annamimi ba zai shiga aljanna ba".
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

(Annabi) Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana ba da labarin cewa annamimi wanda yake cirato zance a tsakanin mutane da nufin ɓata tsakaninsu shi mai cancanta ne ga uƙubar cewa ba zai shiga aljanna ba.

Hadeeth benefits

  1. Annamimanci yana daga manyan zunubai.
  2. Hani daga annamimanci; saboda abin da ke cikinsa na ɓatawa da cutarwa a tsakaknin ɗaiɗaiku da jama'u.