- Mummunan zato ba ya cutar da wanda alamominsa suka bayyana daga gare shi, ya wajaba akan muminai su zama masu basira masu fahimta, kada su yaudaru da munanan mutane da kuma fasikai.
- Abin nufi shi ne gargadarwa daga tuhumar da take zama a cikin zuciya, da kuma nacewa akanta, amma abinda yake bijirowa a cikin zuciya ba ya tabbata to wannan ba'a dorawa da shi.
- Haramta sabubban kyamar juna da yankewa a tsakanin zamantakewar musulmai, na bincike da hassada da makancinsu.
- Wasicci da yi wa musulmi mu'amala mu'amalar dan uwa, a nasiha da kauna.