- Umarni da dukkan abinda 'yan uwantaka ta imani take hukunta wa, da kuma hani daga binda yake kishiyantarta na maganganu da ayyuka.
- Madogarar tsoron Allah ita ce abinda ke cikin zuciya na sanin Allah, da tsoronSa da muraƙabarSa, kuma wannan taƙawar taba fitowa ne daga ayyuka na gari.
- Kaucewa ta zahiri tana nuni akan raunin taƙawa ta zuciya.
- Hani daga cutar da musulmi ta kowace fuska daga fuskoki na magana ne ko aiki.
- Ba hassada ba ne musulmi ya yi burin ya zama tamkar waninsa, ba tare da burin gushewar (ni'ima ba) daga wani, wannan ana kiransa kishi; kuma wannan ya halatta yana taimako akan rigegeniya zuwa ayyukan alheri.
- A ɗabi'ar mutum yana ƙin ace wani ya fishi a wani abu na falaloli, to idan ya so gushewarta daga ɗayan to wannan ita ce hassada, idan kuma ya so rigegeniya to wannan shi ne kishin da ya halatta.
- Idan ya bayyanawa mai siye cewa mai siyarwar ya ha'ince shi ha'inci mai muni a cikin siyansa to wannan ba ya cikin cinikin musulmi akan cinikin ɗan'uwansa; kai wannan yana daga mahukuntar nasiha, amma da sharaɗin niyyarsa ta zama ita ce yi wa ɗan'uwansa mai siye nasiha ba wai cutar da mai siyarwar ba, ayyuka kuwa (ana musu hukunci ne) da niyyoyi.
- Idan musu cinikin ba su yarda da cinikin ba kuma farashin bai tabbata ba to hakan ba ya daga cikin ciniki akan cinikin ɗan'uwansa.
- Kiyayya saboda Allah ba ta cikin ƙiyayyar da aka yi hani a kanta a cikin hadisin, kai shi wajibi ne ma, kuma yana daga mafi amintakar igiyar imani.