- Ba da rashawa yana haramta, da karɓarta da yin hanya zuwa gareta, da taimako a kanta; don abin da ke cikinta na taimakekeniya a kan ƙarya (ɓarna).
- Rashawa tana daga manyan zunubai; domin cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tsinewa mai karɓarta da mai ba da ita.
- Rashawa a shari'a (Alƙalanci) da hukunci ita ce mafi girman laifi, kuma mafi tsanani; don abin da ke cikinta na zalunci da hukunci ba tare da abin da Allah Ya saukar ba.