- Illar haramta giya shi ne maye, dukkan abinda yake sa maye daga kowanne nau'i ya kasance to haramun ne.
- Allah - Maɗaukakin sarki - Ya haramta giya; dan abinda ta ƙunsa na cututtuka da ɓarna masu girma.
- Shan giya a cikin aljanna yana daga cikar jin daɗi da cikar ni'ima.
- Wanda bai kame kansa daga shan giya a duniya ba Allah Zai haramta masa shan ta a cikin aljanna. Sakamako yana zuwa ne daga jinsin aiki.
- Kwaɗaitarwa akan gaggawar tuba daga zunubai kafin mutuwa.