- A cikin hadisin akwai gabatar da uwa, sannan uba, sannan mafi kusanci sai mafi kusanci, gwarwadan darajojinsu a kusanci.
- Bayanin matsayin mahaifa musamman uwa.
- A cikin hadisin ya maimaita yi wa uwa biyayya sau uku; hakan dan girman falalarta akan 'ya'yanta, da kuma yawan abinda take ɗauka na wahalhalu da gajiya da kuma wahalar ciki, sannan haihuwa, sannan shayarwa, abubwan da uwa take kaɗaitaka da shi, sannan ta yi tarayya da uba a cikin tarbiyya.