- Sada zumunci abin la'akari a shari'a shi ne ka sadarwa wanda ya yanke maka daga gare su, ka yi afuwa ga wanda ya zalinceka, ka bawa wanda ya haramta maka, bawai sadarwar fuskanta da sakayya ba.
- Sada zumunci yana kasancewane ta hanyar sadar da abinda zai yiwu na alheri na dukiya da addu'a, da horo da aikin alheri, da kuma hani daga abin ki da makamantansu, da kuma tunkude abinda zai yiwu na sharri daga gare su.