- (Abokan) Zumunci su ne 'yan uwa ta ɓangaren uba da uwa, a duk lokacin da ya kasance mafi kusa, to, ya zama mafi cancanta da sadarwa.
- Sakamako yana kasance ne daga jinsin aikin da aka yi, wanda ya sadar da zumuncinsa da kirki da kyautatawa, Allah Zai sadar da shi a rayuwarsa da arzikinsa.
- Sadar da zumunci sababi ne na yalwar arziki, kuma sababi ne na tsawon rayuwa, duk da cewa ajali da arziki abin iyakancewa ne, sai dai cewa zai iya zama albarka cikin arziki da rayuwa, sai ya yi aiki a rayuwarsa mafi yawa kuma mafi amfani daga abin da waninsa zai aikata, a wata faɗar aka ce ƙarin arziki da rayuwa ƙari ne na haƙiƙa. Allah ne Mafi sani.