- Yanke zumunci laifi ne daga manyan laifuka.
- Sa da zumunci yana kasancewa ne gwargwadon abin da aka yi sabo a kansa, yana banbanta da banbantar wurare da zamaninnika da mutane.
- Sa da zumunci yana kasancewa ne da ziyara da sadaka, da kyautatawa garesu, da duba marasa lafiya, da umartarsu da aikin alheri, da hanasu daga abin ƙi, da makamancin hakan.
- A duk lokacin da yanke zumuci ya zama da mafi kusanci, to, zai zama ya fi tsananin laifi.