- Kwadaitarwa a isar da shari'ar Allah, kuma cewa mutum ya zama dole akansa ya bayar da abinda ya haddace kuma ya fahimta koda ya zama kadan ne.
- Wajabcin neman ilimi na shari'a dan ya samu ga tabbata ga bautar Allah da kuma isar da shari'arSa da inagantacciyar sura.
- Wajabcin tabbaci daga inagancin kowanne Hadisi kafin isar da shi ko yadashi dan kiyayewa daga shiga a wannan narkon mai tsanani.
- Kwadaitarwa akan gaskiyar zance da kuma kiyayewa a Hadisi dan kada ya afka a cikin karya, musamman ma a shari'ar Allah - Mai girma da daukaka -.