/ Wanda ya yi tsayuwar dare a daren Lailatul ƙadari yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa

Wanda ya yi tsayuwar dare a daren Lailatul ƙadari yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya yi tsayuwar dare a daren Lailatul ƙadari yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labari game da falalar tsayuwar Lailatul kadari wacce take kasancewa a goman ƙarshe na Ramadan, cewa wanda ya yi ƙoƙarin yin sallah a cikinta da addu'a da karatun al-ƙur'ani da zikiri, yana mai imani da ita, da kuma abin da ya zo a falalarta, yana mai kwaɗayin sakamakon Allah - Maɗaukakin sarki - da aikinsa, ba don riya ko jiyarwa ba, to, za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa.

Hadeeth benefits

  1. Falalar daren lailatul ƙadri da kwaɗaitarwa a kan tsayuwarsa.
  2. Ayyuka na gari ba'a karɓarsu sai tare da gaskiyar niyyoyi.
  3. Falalar Allah da rahamarsa, cewa wanda ya tsaya (da ibada) a daren Lailatul ƙadri yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa.