- Haramcin azimin ranakun idin ƙaramar sallah da babba da kwanukan Tashriƙ; domin cewa su masu bi ne ga ranar babbar sallah sai dai ga wanda bai samu hadaya ba to azimin kwanukan tashriƙ ya halatta gare shi.
- Ibnu Hajar ya ce: An ce: Fa'idar siffanta ranaku biyun dan nuni ga illa a wajabcin cin abinci a cikinsu, shi ne rabewa daga azimi, da bayyanar cikarsa shi kaɗai da karya azimin abinda ke bayansa, ɗayan kuma saboda yanka wanda ake neman kusanci da yankansa dan a ci daga gare shi.
- An so ga mai huɗuba (liman) a cikin huɗubarsa ya tinatar da abinda yake rataye da lokacinsa na hukunce-hukunce kuma ya kintaci munasabobi.
- Halaccin ci daga abin yanka.