- An so sahur da riko umarnin shari'a da aikata shi.
- Ibnu Hajar ya ce a cikn Fathul Bari: Albarka a cikin sahur tana samuwa ne ta ɓangarori masu yawa, su ne bin sunna, da saɓawa Ahlul kitabi, da ƙarfafuwa da shi akan ibada, da ƙari a cikin nishaɗi, da tunkuɗe munanan ɗabi'u wanda yunwa take taso shi, da kawo sababin sadaka ga wanda yake roƙo a wannan lokacin ko yake haɗuwa da shi akan cin abin ci, da sabbaba zikiri da addu'a a lokacin ana fatan amsawa, da riskar niyyar azimi ga wanda ya rafkana daga gareta kafin ya yi bacci.
- Kyakkyawar koyarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - inda yake haɗa hukunci da hikima; dan ƙirji ya buɗe da shi, kuma a san matsayin shari'a da shi.
- Ibnu Hajar ya ce: Sahur yana samuwa ne da mafi ƙarancin abinda mutum yake samunsa na abin ci da abin sha.