- AlNawawi ya ce: Falalar azimi a tafarkin Allah, shi abin ɗauka ne akan wanda ba ya cutuwa da yin azumin, kuma ba zai salwantar da wani haƙƙi idan ya yi azumin, kuma yaƙinsa ko waninsa ba zai bata muhimman yaƙi da shi ba.
- Zaburarwa da kwaɗaitarwa akan azimin nafila.
- Wajabcin ikhlasi da neman yardar Allah, kuma kada ya yi azimi dan riya ko jiyarwa ko dan wasu manufofin daban.
- Sindi ya ce: Faɗinsa (A tafarkin Allah), za'a iya ɗaukar cewa abin nufi mujarradin gyara niyya, kuma za'a iya ɗaukar cewa abin nufi da shi cewa shi ya yi azimi a halin kasancewarsa mai yaƙi, na biyun shi ne abin gaggawar (manufa).
- Ibnu Hajar ya ce: Faɗinsa:
- (Kharif saba'in) Kharif wani lokaci ne sananne a shekara, abin nufi da shi a nan shekarar (gaba ɗayanta), kuma keɓance Kharif (Kaka) da ambato banda ragowar lokutan - zafi da sanyi da damina -; domin cewa Kharif (Kaka) ya fi ragowar lokutan kyau domin kasancewarsa ana tsinkar 'ya'yan itatuwa a cikinsa.