- Kwaɗaitarwa da ribatar mafifitan lokuta da ayyuka na gari.
- AlNawawi ya ce: A cikin wannan hadisin: Cewa an so a yi ƙari daga ibadu a cikin goman ƙarshe na Ramadan, kuma an so raya dararensa da ibadu.
- Yana kamata ga bawa ya zama mai kwaɗayi akan iyalansa da umartarsu da yin ibada, kuma ya yi haƙuri akansu.
- Aikata alherai yana buƙatuwa zuwa ƙudirin niyya da haƙuri da dagewa.
- AnNawawi ya ce: Malamai sun yi saɓani a ma'anar (ya ɗaure gwabso) an ce: Shi ne ƙoƙari a cikin ibadu ƙari akan al'adarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a waninsa, kuma ma'anarsa: Zage damtse a cikin ibadu, ana cewa; Na ɗaure gwabso na dan wannan al'amarin, wato: Na zage damtse gare shi na yi ƙoƙari, an ce: Shi kinaya ne game da nisantar iyali dan shagaltuwa da ibadu.