- Ingancin azimin wanda ya ci ko ya sha akan mantuwa.
- Babu zunubi akan wanda ya ci ko ya sha akan mantuwa; domin cewa shi bada zaɓinsa ba ne.
- Sauƙin Allah ga bayinSa da sauƙaƙa musu da ɗauke wahala da ƙunci daga gare su.
- Mai azimi ba ya karya aziminsa da wani abu daga abubuwa masu karya azimi sai idan sharuɗɗa uku sun cika:
- Na farko: Ya zama masani, idan ya kasance jahili bai karya azimi ba.
- Na biyu: Ya zama yana mai tinawa, idan ya kasance yana mai mantuwa, to aziminsa ingantacce ne kuma babu ramuwa akansa.
- Na uku: Ya zama yana mai zaɓi ba abin tilastawa ba shi ne ya ci abinda yake karya azimi da zaɓinsa.