Wanda ya azumci Ramadan yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya azumci Ramadan yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa".
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labari cewa wanda ya azumci watan Ramadan yana mai imani da Allah, yana mai gasgatawa da wajabcin azumin da abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi tanadi na gwaggwaɓan ladaddaki da sakamako, yana mai nufin zatin Allah - Maɗauakakin sarki - da shi ba don riya ko jiyarwa ba, za'a gafarta masa zunubansa da suka shuɗe.
Hadeeth benefits
FALALAR TSARKAKE NIYYA DA MUHIMMANCINSA A AZUMIN RAMADAN DA WANINSA NA AYYUKA NA GARI.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others