- Abinda ya kamata a shagalta da mafi muhimmancin abinda ake buƙatuwa zuwa gare shi, da barin abin da ba'a buƙatuwa zuwa gare shi a wannan lokaci, da barin shagaltuwa da tambaya daga abinda bai afku ba.
- Haramcin tambayar da wataƙila ta kai zuwa ƙulle mas'aloli, da buɗe ƙofar shubuhohi masu kaiwa zuwa yawan saɓani.
- Umarni da barin dukkan abinda aka hana; domin babu wata wahala a barinsu, saboda haka hanin da aka ya yi zama gamamme.
- Umarni da aikata abinda aka yi umarni da shi gwargwadan iko; domin zai iya lizimtar da wahala ko a gajiya a aikata shi; saboda haka umarni da shi ya zama akan gwargwadan iko.
- Hani akan yawan tambaya, haƙiƙa malamai sun raba tambaya gida biyu: Ta ɗayansu: Wadda take kasancewa ta fuskar koyarwa ga abinda ake buƙatuwa zuwa gare shi na al'amarin addini, to wannan an yi umarni da ita, daga wannan nau'in tambayoyin sahabbai suke.
- Na biyu: Wadda ta kasance ta fuskar ta'annuti da ɗorawa kai to wannan ita ce wacce aka hana.
- Gargaɗin wannan al'ummar daga saɓawa annabinta, kamar yadda ya afku a cikin al’ummun da suka gabata.
- Yawan tambaya yana daga abinda ba'a buƙatuwa zuwa gare shi, kuma saɓawa annabawa sababi ne na halaka, musamman ma a cikin al'amuran da kaiwa gare su ba zai yi wu ba, misalin: Mas'alolin gaibun da babu wanda ya sansu sai Allah, da halayen ranar Alkiyama.
- Hana yin tambaya a mas'aloli masu tsanani, Auza'i ya ce: Lallai Allah idan Ya yi nufin haramtawa bawanSa albarkar ilimi sai Ya jefawa harshensa galaɗi mai yawa, haƙiƙa na gansu (su ne) mafi ƙarancin mutane a ilimi. Ibnu Wahab ya ce: Na ji Malik yana cewa: Gaddama a cikin ilimi tana tafiyar da hasken ilimi daga zuciyar mutum.